Sanarwar doka
I – Bayanin doka
1. Mawallafi
France Médias Monde
Société anonyme (French public limited company) mai jari 6,947,560 euros
Rijistar Nanterre Trade and Companies: 501 524 029
Ofishin da aka yi rijista: 80, rue Camille Desmoulins
92130 Issy Les Moulineaux
France
Darektan Wallafawa: Marie-Christine SARAGOSSE
Hanyar tuntuɓa: Rubuta mana ko applis@rfi.fr applis@mc-doualiya.com support-app@france24.com
Allonsauyin France Médias Monde: +33 1 84 22 84 84
2. Masaukan yanar-gizo
Claranet
19 Rue Michel le Comte
75003 Paris
France
Wayar: +33 1 70 13 70 00
Akamai
12 rue Oradour-sur-Glane
75015 Paris
France
II – Sharuɗɗan Anfani na Gabaɗaya
1. Dalili
Dalilin waɗannan Sharuɗɗan yin Amfani na Gaba ɗaya (wato “GTU”) shi ne fayyace da gano sharuɗɗa da hurimin da France Médias Monde ke samar da duk sassan yanar-gizon da suke ƙirƙira (wato “Sassan yanar-gizo”) domin masu amfani, da kuma sharuɗɗan da ke kula da isa da ziyarar mai amfani ga waɗannan Sassan yanar-gizon. Za a iya isa ga Sassan yanar-gizon ta adireshin da ke tafe:
- https://www.francemediasmonde.com
- https://www.francemm.com
- https://www.rfi.fr
- https://www.rfi.ro
- https://gastronomie.rfi.ro
- https://muzica.rfi.ro
- https://europaplus.rfi.ro
- https://generatia30.rfi.ro
- https://rural.rfi.ro
- https://webdoc.rfi.ro
- https://www.france24.com
- https://observers.france24.com
- https://observers.rfi.fr
- https://howtowatch.france24.com
- https://www.mc-doualiya.com
- https://www.infomigrants.net
- https://francaisfacile.rfi.fr
- https://musique.rfi.fr
- https://mondoblog.org
- https://appafrique.rfi.fr
- https://www.rfi-instrumental.com
- https://www.rfiadvertising.com
- https://www.ecouterlemonde.net
- https://academie.francemm.com
- https://www.cfi.fr
- https://www.ac.cfi.fr
- https://www.24hdansuneredaction.com
2. Sharhi
Domin waɗannan dalilan GTU:
“Sharuɗɗan Amfani na Baiɗaya” ko “GTU” na nuni da dokokin da aka samar a nan, waɗanda Mai amfani ya amince kuma suke kula da isa da amfani da Sassan yanar-gizon.
“Jawabi” na nufin rubutun da Maiamfani ya rubuta domin yin jawabi a game da ƙunshin batun (cf. sharhi a ƙasa). Masu amfani da Intanet za su iya ganin Jawaban Mai amfani da ya ziyarci Sassan yanar-gizon.
“Asusun Maiamfani” na nufin sararin da ke a Sashen yanar-gizo da aka tanadar ma Mai amfani ta hanyar shiga yanar-gizo da kalmar sirri, waɗanda, musamman, suke ba shi/ta damar samun wasiƙun labaru.
“Ƙunshi” na nufin ƙunshi da abubuwa da Sassan yanar-gizo suka ƙunsa, musamman hotuna, surori, rubuce-rubuce, labaru, kwatance, saututtuka, bidiyo, da Na’urar kunna bidiyon da Na’urar bkunna Sauti (cf. sharhi a ƙasa).
“Ƙunshin Mai amfani” na nufin kowame irin rubuce-rubuce, kwatance, hotuna, surori, saututtuka da bidiyo da Mai amfani ya samar a Sararin Gudunmawa.
“Sararin Gudunmawa” na nufin duk shafukan da aka samar ma Mai amfani a Sassan yanar-gizo inda za su iya jawabi a kan Ƙunshin.
“Na’urar Kunna Bidiyo” na nufin shirin sofwayan da ke bayar da damar kunna Ƙunshin bidiyo. Ana iya fitar da Na’urar kunna Bidiyo kuma ana iya bari waɗansu wanda aka taɓa bai wa dama ta wata yarjejemiya su yi aiken Ƙunshi a Sassan yanar-gizonsu a ƙarƙashin hurimin da aka shimfiɗa a wannan GTU. Domin ba ku kyakkyawan ƙwarewar kallo, Mai kunna Bidiyo da France Médias Monde ke amfani dashi shine sigar mai kunna bidiyo ta YouTube wacce Sharuɗɗan Amfani da YouTube ke aiki dashi. A matsayin wani ɓangare na wannan sabis ɗin kuma tare da izininka, YouTube na iya tattara bayanan sirri don dalilai na auna masu sauraro, shawarwarin abun ciki da tallace-tallace da aka yi niyya, ƙarƙashin sharuɗɗan Manufofin Sirri na Google.
“Na’urar kunna Sauti” na nufin shirin sofwayan da ke bayar da damar kunna Ƙunshin sauti. Ana iya fitar da Na’urar kunna Sautin kuma ana iya bari waɗansu wanda aka taɓa bai wa dama ta wata yarjejemiya su yi aiken Ƙunshi a Sassan yanar-gizonsu a ƙarƙashin hurimin da aka shimfiɗa a waɗannan GTU.
“Sabis-sabis” na nufin sabis-sabis ɗin da za a iya isa gare su a kan/ko daga Sassan yanar-gizon kuma France Médias Monde ne suka ƙirƙiro.
“Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amala” na nufin sabis-sabis ɗin da wasu abokan ma’amala suka ƙirƙiro da za a iya iso gare su a kan/ko daga Sassan yanar-gizon, musamman ta kafofi da aka saka a ɓangarori daban-daban.
“Sassan yanar-gizo” na nufin sassan yanar-gizon da France Médias Monde suka ƙirƙiro, kamar yadda aka jera su a layin farko na waɗannan sharuɗɗa, haka kuma da duk sauran sigoginsu ba tare da la’akari da yadda ake isa gare su ba (sassan yanar-gizon wayar hannu,wayar hannu da/ko manhajar tablet musamman).
“Ma(i/su) amfani”: na nufin mutumin da ke ziyartar Sassan yanar-gizon.
3. Amincewa da GTU
Duk wani amfani da Sassan yanar-gizon na faruwa ne a ƙarƙashin waɗannan GTU, da ke da nufin samar da sharuɗɗa da hurumin yin amfani da Sabis-sabis da Ƙunshin da aka samar a Sassan yanar-gizon.
Isa ga Sassan yanr-gizon na nufin amfani da kuma amincewa da waɗannan GTU. GTU ɗin da ke amfani su ne waɗanda ke tilasta doka a ranar duk sanda Mai amfani ya shiga Sassan yanar-gizon.
An fayyace cewa France Médias Monde na iya gyara GTU ɗin a kowane lokaci domin su saba da bunƙasar Sabis-sabis da dokokin yanzu. Ana sanar da Masu amfani game da waɗannan sauye-sauye cikin sauƙi ta hanyar abin da suka wallafa a kan layi. Daga nan kuma, ana ɗaukar su a matsayin ƙarɓaɓɓu ba tare da wani tanadi daga kowane Mai amfani da ke isa ga Sassan yanar-gizon bayan an wallafa ba. Bayan haka, ana ba ma Mai amfani shawara da ya bincika su a kowace ziyara domin sanin sabuwar sigar da aka samar a Sassan yanar-gizon.
4. Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amala
Sassan yanar-gizon na ba da damar isa ga Sabis-sani ɗin Abokin Ma’amala ta kafafen da aka saƙala a ɓangarori daban-daban na Sassan yanar-gizon zuwa sassan yanar-gizo, ƙunshi, da sabis-sabis da abokan ma’amalar suka ƙirƙiro. Za a iya isa ga Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amala musamman ta danna alamomin talla (farfajiya, bidyo, da sauransu).
Mai amfani ya tabbatar cewa waɗannan Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amalar ba su da alaƙa da France Médias Monde. Saboda haka, duk wani amfani da Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amalar ta Sassan yanar-gizon zai kasance yana da alaƙa da sharuɗɗan amfani da/ko fayyacacciyar sayayya ta ko wane Abokin Ma’amala da kuma aƙidar kariyar bayanansu.
France Médias Monde ba za su ɗauki alhakin ƙunshin da za a iya isa ciki ba, duk wasu abubuwa, bayanai da aka tuntuɓa ko kasuwanci da aka yi a kan Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amala ba. Haka kuma, France Médias Monde ba sa ba da garanti a kan sharuɗɗa da hurumin aikin waɗannan dokoki na yanzu da mawallafin Sabis-sabis ɗin Abokin Ma’amala ya samar, wanda su ke da alhaki.
5. Masu amfani
5.1 Asusu-asusn Mai amfani
Kyauta ne isa ga Sassan yanar-gizon kuma ba sai ka yi rijista ba.
Har wa yau, wasu sabis-sabis da aka samar a kan Sassan yanar gizon (kamar aika wasiƙun labaru) na iya kasancewa masu alaƙa da rijistar Mai amfani, amfani da Asusun Mai amfanin(shi/t)a domin gane shi/ita.
Yayin da ya/ta ke ƙirƙirar Asusun Mai amfani, za a buƙaci Maiamfani da ya/ta zaɓi ID na mai-amfani da wata kalmar sirri mai alaƙa, waɗanda suke mallakakku matuƙar da sirri. Za a samar ma Mai amfani wani fam na rijista domin samar da wasu bayanan kai ga France Médias Monde wanda yake wajibi ko mai zaɓi kamar yadda fam ɗin ya nuna Idan Mai amfanin bai samar da bayanan da aka wajabta ba, ba za a ƙirƙiri wannan Asusun Mai amfanin ba.
Ana karɓara wannan bayanin kai ne kai tsaye daga Mai amfani domin gane su cikin sauƙi yayin da za su shiga sashen nan gaba da kuma samar masu da ƙarin sabis-sabis da/ko isa ga wasu abubuwa. Ana adana bayanan kai ne tare da amincewar Mai amfani kuma suna da alaƙa da tsari kamar yadda aka samar a Doka ta 10 ta waɗannan GTU. Ana adana su ne daga ranar da aka ƙirƙiri Asusun Mai amfanin har tsawon lokacin da ake amfani da Sabis-sabis ɗin. Bayan ranar da France Médias Monde suka cire rijistar saboda rashin ziyarar Mai amfani ko saboda da buƙatar Mai amfani cewa a cire Asusun, za a adana bayani har tsawon watanni 13.
5.1.1 Kariyar Yara
Idan Mai amfanin ya/ta kasance yaro/yarinya mai zaman kan(sa/ta), kuma ya/ta sanar da kuma tabbatar da samun izini shiga Sassan yanar-gizon daga mahaifa ko wani mai iko kamar mahaifa a kan shi/ita. Mahaifan ko mai iko kamar mahifan zai kasance garanto a kan tabbatar da bin dokokin GTU yayin da yaron ko yarinya ke amfani da Sassan yanar-gizon.
Ana gayyatar Mahaifa (ko masu iko kamar mahaifa) su saka ido kan yadda yaransu ke amnfani da Sabis-sabis ɗin (masu kula da su) da kuma cewa Sabis-sabis ɗin na jama’a masu yawa ne da kuma cewa a matsayin su na masu kula, haƙƙin mahaifa ne su ƙayyade wane Sashen yanar-gizo ne ya dace ko rashin dacewa da yaransu da kuma kula da yadda ake amfani da su. Domin ƙarin bayani game da tacewa, musamman domin kare yara, France Médias Monde na ba ma mahaifa shawara su tuntuɓi mai samar da sabis ɗin Intanet ɗinsu kuma su garzaya zuwa shafin da ke tafe: https://www.education.gouv.fr/cid141/la-protection-des-mineurs-sur-internet.html
An fayyace cewa ba a ba ma yara izini su ƙirƙiri wani Asusun Mai amfani ba.
5.1.2 ID na Mai amfani domin Sabis-sabis ɗin Wani
Wataƙila sai an yi amfani da ID na Mai amfani domin sabis-sabis ɗin wani kamar Facebook, Twitter, Google + da kuma LinkedIn domin isa ga wasu ayyuka ko sabis-sabis.
Dole Mai amfani ya shiga yanar-gizo da ID na mai amfani da aka fayyace ma sabis-sabis ɗin wani domin duka ayyukan hanyoyin sadarwar ma’amala da suka haɗa da cuɗanya da sabis-sabis ɗin wani.
Sharuɗɗan amfani da kuma aƙidar kariyar bayanan kai da aka fayyace ma kowane sabis ɗin wani ne ke kula da ƙirƙira da amfani da waɗannan asusun da kuma bayanin kai da Mai amfani ya samar zuwa ga waɗannan sabis ɗin waɗansu, don haka wannan ya fitar da France Médias Monde daga ɗaukar kowane alhaki a wannan ɓangare.
5.2 Sararin Gudunmawa
5.2.1
Masu amfani na da damar jawabi a Ƙunshin da aka aika a Sassan yanar-gizon (wato “jawabin”) da/ko su aika rubutu, bidiyo,saututtuka, surori da/ko hoyuna (wato “Ƙunshin Ma’anfani”). Duk wani mai amfani da Intanet da ya ziyarci waɗannan Sassan yanar-gizon zai iya ganin waɗannan Jawaban da Jawaban Mai amfani
France Médias Monde ba sa gudanar da wani bincike a kan Ƙunshin Mai amfani da/ko Jawabi da Masu amfani suka aika gabanin haka, wanda su suke da alhaki a kan ƙunshin Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfanin da suka samar.
Babu wani dalili da zai sa France Médias Monde su zama masu alhakin Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfani da wani mai amfani ya aika a kan layi wanda ba ya da ikon da ake buƙata domin wannan aiken.
Duk wani Mai amfanin da ya aika da Jawabai da/ko Ƙunshin Mai amfani a kan Sassan yanar-gizon yana ba France Médias Monde ikon adanawa, sake bugawa da wakiltar wannan Jawabi da/ko Ƙunshin Mai amfani a kyauta kuma ba tare da wani sharaɗi ba, har na tsawon duk lokacin damar ƙwazon kadarori da aka wallafa.
An fayyace cewa saboda da dalilan fasaha, za a iya sake fasalin wani Ƙunshin Mai amfani domin ya dace da Doka ta 7.3 ta waɗannan GTU (musamman ma salon rubutun, girman rubutun da kuma tada-baƙi). Ba za a yi wani canje-canje sosai ba ga Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfani ba tare da mai amfani ya amince a rubuce ba wanda shi ne marubucin Ƙunshin Mai amfanin.
5.2.2
Mai amfanin ya sha alwashin ba zai aika da Ƙunshin Mai amfani da Jawabai da ba su da dace da dokokin yanzu na France ba kuma waɗanda:
- suka saɓa ma zaman lafiya da natsuwa
- saɓa ma sirrin wani
- take haƙƙin rufin asirin samar da bayani ga ƴan jarida
- saɓa ma rufin asirin sana’a
- nufin bambancin launin fata, addini da ƙabilanci, bayyanannun alamomi ko naƙasar mutum har sai waɗannan kwatancen suna da muhimmanci wajen fahimtar bayanin
- na bayar da gudunmawa wajen yaɗa wani aiki da Intellectual Property Code ya kare ba tare da samun izini ba tun farko
- zagi, ƙasƙantawa, wulaƙanci, saɓa ma mutuncin mutum, ƙima da girma, furucin bambancin launin fata ko gasar da ba ta dace ba
- saɓa ma girman wanda ake magana a kai
- tozarta waɗanda suka gamu da wulaƙanci ko barazanar fyaɗe, har sai wanda abin ya shafa ya amince a rubuce
- ƙarfafa yaɗa bayanai da suka shafi gane wanda abin ya shafa ko tozarta ƙaramin yaro/yarinya
- goyon bayan mugayen ayyuka da/ko laifuffuka masu sa amfani da haramtattun abubuwa ko sa kisan kai
- hana wasu laifuka, musammman kisa, fyaɗe, laifukan yaƙi, laifuka a kan ɗan’adam
- na banbancin launin fata, ƙiyayyar juna, kiyayyar baƙi, goyon bayan komunusanci, batsa ko alfahasha, ko yaranta
Bugu da ƙari, Masu amfani sun sha alwashin rubuta Jawabai da/ko Ƙunsin Mai amfani wanda:
- suka dace kuma suke da alaƙa da batun da ake tattaunawa
- suke da sauƙi wajen karantawa da fahimta, a kauce ma tauye haruffa da kuma “harsunan Saƙonni”
- a kauce ma yawan amfani da manyan haruffa waɗannda za a fahimta kamar fishi
- ba yarfe ba ne ko watsi (maimaita aika saƙo ɗaya).
5.3 Kulawa da Sararin Bayar da Gudunmawa
France Médias Monde na iya, amfani da ikonsu, su share duk wani Jawabi da/ko Ƙunshin Mai amfani bayan an aika a Sashen yanar-gizon idan wannan Jawabi da/ko Ƙunshi Mai amfani ya saɓa ma bin Doka ta 5.2.2 da, kuma kauce ma dokokin France na yanzu.
6. Kadarar Ilimi
6.1 Ƙunshi da Abubuwan Sashen Yanar-gizo
An tandi da kuma kare abubuwan da Sassan yanar-gizo suka ƙunsa, kamar rubutu, saututtuka, bidiyoyi, kiɗa, shirin sofwaya, tarin-bayanai, alamomi, sunayen kamfani, da wasu abubuwa da aka sake samarwa a ƙarƙashin dokar kadarar ilimi (musamman damar kwafa, wasu dama masu alaƙa da dokar sunan kamfani). Waɗannan kararrun abubuwan su ne kadarar France Médias Monde da/ko abokan ma’amalarsu.
A karkashin dokar dake da nasaba da kare fasahar jama’a, duk wani yunkurin sake amfani (ciki harda saukewa, ko wallafawa, da sauransu) wani sashe ko kuma daukacin aikin da akayi, an haramta mallakarsa ko fassara shi ko sake masa fasali da/ko kuma sauya shi zuwa wani shafi na daban ko kuma duka daga cikin bayanan da akayi a sama. Akwai haramci sosai akan dauka ko ajiya ko amfani ko tsakura ko sake wallafawa kai tsaye ko kuma ta wata hanya, na din-din-din ko kuma na wucin gadi, duka ko kuma wani bangare ba tare da samun umarni ba, ta kowacce hanya da kuma ko wanne irin dalili, kai tsaye ko kuma a fakaice, musamman abinda ya shafi horo ko ci gaba da ayyukan duk wata manhaja, tsari da kuma fasahar kirkirarriyar basira. Wannan sharadi ya kunshi, sharadin doka mai lamba L122-5-3 na dokokin kare fasahar jama’a ta tanada. An kuma bayyana haramcin wannan tsari ta amfani da wata hanyar daukar bayanai kai tsaye ta hanyar "tdm-reservation": 1 a cikin rumbun /.well-known/tdmrep.json a cikin shafukan. France Médias Monde na iya amfani da duk wata fasaha domin hana amfani da ayyukan da aka dora a shafukanta ta hanyar amfani da na’urar mutum mutumi ko kuma duk wata fasaha don kare mallakarta, musamman wajen gabatar da horo ko kuma bunkasa hanyar amfani da na’ura koyarwa ko kuma kirkirarriyar basira. France Medias Monde na iya kama wani mutum ko wasu kungiyoyi dake amfani da wadannan hanyoyi ba bisa ka’ida ba da laifin satar fasaha.
France Médias Monde yana ba ma Mai amfani damar da ba za a iya turawa zuwa ga wani daban ba, kyauta, mara wariya, na kai da kuma damar rufin asiri domin yin amfani da Sabis-sabis da Sassan yanar-gizon domin amfanin kai da rufin asiri, tare da tsananin biyayya ga sharuɗɗan amfani da aka shinfiɗa a waɗannan GTU.
6.2 Sunanyen Kanfani
Sunayen kamfanin France Médias Monde da na abokan ma’amalarsu, tare da alamomi a kan Sassan yanar-gizo, sunayen kanfani masu rigista ne asboda haka suna da kariya a ƙarƙashin dokar kadarar kanfanoni (Doka ta L 713-2 et seq. ta French Intellectual Property Code). An haramta yin amfani da waɗannan sunayen kanfanin ko alamomin, har sai mamallakinsu ya bayar da damar yin haka. Duk wani yin amfani da wani kararren sunan kanfani ko alama ya saɓa ma dokar damar ƙwafa kuma hakan na iya sanadiyar hukunci a kotuna.
6.3 Gudunmawar Mai amfani
Kowane Mai amfani ya tabbatar ma France Médias Monde cewa shi/ita na da adamar da ta dace domin aika Jawabai da/ko Ƙunshin Mai amfani a kan Sassan yanar-gizon.
A sanidiyar haka, duk Masu amfani sun tura ma France Médias Monde damar sake samar, wakilci, kwafa, sauya kama, sake tsari, sake wallafa, sadarwa, rabawa, sabawa, da kuma yin amfani da gaba ɗaya ko wani ɓandare na Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfani a Sassan yanar-gizon da/ko shafukan sadarwa na France Médias Monde, da kuma wasu siga ba tare da la’akari da yadda ake shigar da su ba, kyauta, da kuma wata matsaya da ba a ware ba, a duk lokacin da aka kare damar kadarar ilimi da ke da alaƙa da Jawabansa da/ko Ƙunshin Mai amfaninsa.
Ana tura damar zuwa duniya domin kowane irin amfani a duk labaru da kuma duk wata hanyar watsa labaru da aka sani ko ba a sani ba.
Mai amfanin ya sheda da kuma amincewa cewa za a iya sake tsarin wasu Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfani domin dalilai na fasaha ne kawai; Don haka Mai amfanin ya bayar da damar daidaitawar. Babu wani canji da za a yi ma Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfanin ba tare da amincewar Mai amfanin ba kamar yadda Doka ta 5.2, ta tanada.
Mai amfanin ya sheda da kuma amincewa cewa ba za a yi amfani da Jawaban da/ko Ƙunshin Mai amfani daga France Médias da zai zama sanadin biyan wani kuɗin fansa ba.
7. Kafofi
7.1 Kafofi masu sauƙi da miƙaƙƙun kafofi
Kafa mai sauƙi na nufin wata kafa da ke ba da damar isa ga shafin gida na wani daga cikin Sassan yanar-gizon.
Miƙaƙƙiyar kafa na nufin wata kafa da ke ba da damar isa ga takamamman shafi daga cikin Sassan yanar-gizon.
Duk wata ƙirƙirar Mai amfani da kafofin a ɗaya daga cikin Sassan yanar-gizon na nufin cewa Mai amfanin ya samu damar da ta dace daga masu ba da damar domin zancen bainar jama’a na Ƙunshin da ya shafa da, idan zai yiwu, ya biya wani albashi da ke da alaƙa.
An faɗi cewa France Médias Monde na zaman kai ne daban da sassan yanar-gizon da ke da kafa mai suƙi da aka ƙirƙira a kan su kuma ba su da alhakin wallafa ko ƙunshin da aka wallafa a waɗancan sassan yanar-gizon.
7.2 Na’urar kunnawa
Na’urar kunna bidiyo da/ko na’urar kunna sauti da aka saka a sashen yanar-gizon wani na samar damar isa ga Ƙunshin bidiyo da/ko sauti na ɗaya daga cikin Sassan yanar-gizon ta fitar da shi a wani firem a sashen yanar-gizon ko ta samar da hanyar shiga ɗaya ko fiye daga cikin Ƙunshin.
An haramta ɓoyayyen Na’urar-Kunna-Bidiyo da/ko Na’urar-Kunna-Sauti ba tare da izinin France Médias Monde a rubuce ba.
7.3 Kafofi daga Sassan yanar-gizo
Kafofi da Sassan yanar-gizo suka ƙunsa na iya kai wa ga wasu sassan yanar-gizo. Masu amfani su ke da alhaki na ziyara ga ire-iren waɗannan Sassan yanar-gizo na wani. Ba za a ɗaura ma France Médias Monde alhakin samar ma Maiamfani da wannan kafa ba da kuma ƙunshin sassan yanar-gizon wani. Babu wani dalili da zai sa Mai amfani ya ɗaura alhakin ga France Médias Monde domin ɓaci da aka samu ta sandiyar yin amfani da sassan yanr gizo na wani da ake shiga daga Sassan yanar-gizon.
8. Shawarwari na Musamman ga Masu amfani na Ƙasa da Ƙasa
France Médias Monde na bari a samu isa ga Sassan yanar-gizon daga kowace ƙasa, dangane da dokar cikin ta yanzu da duk wata taƙaitawa da aka saka. Duk wani Mai amfani da ke isa ga Sassan yanar-gizon daga wata kwamfuta a wajen ƙasar Faransa ya tabbatar cewa ya/ta karanta, fahimci da amincewa ba tare da iyaka ba game da sharuɗɗan GTU da kuma alwashin bin dokokin cikin gida da duk wata iyakancewa a ƙasar da ake magana.
Ba za a sami isa ga wani Ƙunshi a kan Sassan yanar-gizon daga wasu ƙasashe ba, wannan kuwa yana da alaƙa ne da taƙaitawar iyakoki da masu hakki ko taƙaitattun hakkokin yaɗawa suka gindya. Saboda haka, Masu amfani da suka isa ga Sassan yanar-gizo daga kwamfutoci da suke cikin waɗannan ƙasashe da aka ware an haramta masu amfani da duk wata na’ura aka tsara don bin-sawun da kaucewa matakan samun isa ga wannan ƙunshi daga waɗannan ƙasashe.
9. Alhaki
9.1 Iso ga Sassan Yanar-gizo da Sabis-sabis
Ana samun iso ga Sassan Yanar-gizon da Sabis-sabis sa’o’i ashirin da huɗu a rana da kuma kwanaki bakwai a mako. France Médias Monde za ta yi iya iyawarta wajen bayan da tabbaci na samun iso ga Sassan Yanar-gizon da Sabis-sabis. Kodayake, ba za a riƙe France Médias Monde da alhaki na haɗarin katsewa ko rashin aiki daidai da ya danganci haɗi, kulawa da ayyuka, sabuntawar gyara, hanyar sadarwa da kuma/ko cunkoson tsarin bayani, shisshigi daga wasu mararsa iziki da kuma gurɓatawa ta hanyar watsa duk wasu ƙwayoyin cutar a kan hanyoyin sadarwar da aka ce da kuma sabis-sabis, yajin aiki na ciki ko waje, rashin saiti yadda ya dace ko amfani da kwamfuta daga wani Mai amfani ko wani sauran dalili na ciki wajen ikonta.
Ta yiwu ba za a riƙe France Médias Monde da alhakin idan katsewa ko taɓarɓarewar ingancin Sassan Yanar-gizon da Sabis-sabis ya auku a sanadiyyar wani dalili daga Ubangiji ba. Ana la’akari da abin da ya faru a sanadiyyar wani dalili daga Ubangiji mai dalili ko marar dalili kamar yadda dokar Faransa ta bayyana da kuma tsarin dokar Kotun Cassation ta Faransa.
9.2 Ƙunshiya Gyara
France Médias Monde ta yi alwashin aiki iya iyakawarta wajen bayar da tabbaci na gaskiya da daidaiton bayani da yake samuwa a kan Sassan Yanar-gizo, amma ba zai ɗauki alhakin rashin daidaitonsa, ko amfani da fassarar da ta samar ga Mai amfani ba.
Saboda haka, ba za a riƙe France Médias Monde da alhaki ga duk wata lalacewa na kai tsaye ko a kaikaice, ƙari da gangan ko bisa haɗari, da ya auku a sanadiyyar amfani da Sassan yanar-gizo ko duk wani bayani da aka samu daga Sassan yanar-gizon ba.
France Médias Monde ita ke da alhaki na haɓakawa da kuma/ko gyare-gyare ga Sassan yanar-gizon da kuma Sabis-sabis ɗinsa a kowane lokaci ba tare da sanarwa ba gabani.
Galibi, Mai amfani ba ya riƙar France Médias Monde game da duk wta buƙata ko aiki da wani ya yi da kuma yiwar sakamakon sha’anin kuɗi, ta la’akari da ko da ya auku a sanadiyyar aikinsa/ta kai tsaye ko kaikaice, ko ya auku sanadiyyar amfani da Sassan yanar-gizon daga Mai amfani da kuma duk wani keta dokar GTU ko tsare-tsaren doka na yanzu da kuma sa France Médias Monde ajiye wasu kuɗi don biyan diyya dangane da duk wata ƙara da ta haɗa da yanke hukunci.
10. Asirce Bayanai
France Médias Monde tana gayyatar Mai amfani da ya yi bitar Aƙidar Kariyarta don bayanai kai da kuma mutunta sirri, wanda yake samuwa ta hanyar da take tafe: Bayanai mallakar kai da kuma manufofinta game da kukis ta hanyar mahaɗin da ke zuwa: Kukis.
Waɗannan dokoki suna bayyana asali da kuma yanayin bayanan da France Médias Monde ta karɓa a yayin da Mai amfani yake burauzi da kuma/ko amfani da sabis-sabis da aka samar a kan Sassan yanar-gizon da kuma manhajojin France Médias Monde, dalilan karɓar bayanan da kuma hakkin Mai amfani ga waɗannan bayanai bisa la’akari da dokoki a kan Kariyar bayanan kai da suka shafi ƙasar Faransa da Turai.
11. Samarwar Ƙarshe
Waɗannan GTU sun ta’allaƙa ne da fashin baƙi da ya dace da dokar Faransa. Duk wani saɓani da ke gudana da ya shafi fassara, aiwatarwa ko zartar da waɗannan GTU waɗanda ba a warware ba ta hanyar sulhu cikin kwanaki talatin (30) bayan sanarwar saɓani ta wasiƙa mai rajista da kuma tabbatar da karɓarta, za a miƙa shi ne zuwa iko na musamman na kotunan Nanterre (Faransa).
Idan aka tabbatar da wani ɓangare na samar da waɗannan GTU ba halattacce ba, ko marar inganci ko bai dace ba bisa kowane dalili, za a bayyana sharaɗin ko sharuɗɗan da ake magana a kai a zaman marasa inganci kuma za a riƙe ragowar sharuɗɗan cikin cikarsu da kuma amfani da ci gaba da aiwatar da su.
Babu wani dalili na rashin aiwatarwa ko rashin wani kuka na aiwatarwa na wata doka kowace iri a cikin waɗanann GTU ko na duk wani hakki kowane iri, daga France Médias Monde da za a iya fassara shi da irin wannan doka ko hakki, sai dai idan France Médias Monde ta yarda a rubuce.